Labaran Wasanni
Wasannin Matasa na kasa NYG: ‘yan wasan Kano na cikin mawuyacin hali
Tawagar ‘yan wasan jihar Kano ta matasa ‘yan kasa da shekaru 15, na cigaba da fuskantar Kalubale na kunci , matsi da rashin sanin kaka nikayi sakamakon halin da suka tsinci kansu na rashin masauki a birnin Ilorin na jihar Kwara.
‘Yan wasan da zasu wakilci jihar ta Kano, a wasannin matasa na kasa karo na 06, da zai gudana a Jami’ar Ilorin , na cigaba da gararamba a cikin Jami’ar , inda wasu daga cikin su suke kwana a motocin da suka kawo su wasu kuma a harbar Masallaci da wajen wankin motoci.
Tun bayan saukar ‘yan wasan rashin samun masauki da kuma daukar matakan da suka dace daga jami’an hukumar wasanni ta jiha, yasa ‘yan wasan na cikin yanayin rashin jin dadi da hakan zai haifar da koma baya ko tsaiko ga nasarar da zasu iya samu a wasannin da zasu fafata.
Tuni dai bincike ya tabbatar da cewar ‘yan wasa 10 ne daga jihar ta Kano zazzabi ya kwantar , sakamakon doguwar tafiya zuwa Ilorin daga Kano , da kuma halin da suke ciki na rashin masauki.
Ko a Laraba 13 ga Oktoba kamar yadda wani Jami’i da ya bukaci a sakaye sunan sa ya bayyana an dau ‘yan wasan zuwa Kwalejin fasaha ta Ilorin da Niyyar sama musu masauki sai dai hakan bata samu ba sakamakon rashin tsaftar gurin da za’a kaisu da rashin ruwa da na wutar Lantarki da hakan ya kara sa zirga zirgar ‘yan wasan ta karu da tafiyar Kilomita 50 na kai kawo tsakanin Kwalejin zuwa Jami’ar ta Ilorin.
Haka zalika , bincike ya ya tabbatar da cewar kungiyar Zari Ruga ta Rugby ta biya kudi naira 10,000 na wani kuntataccen daki don samun saukar ‘yan wasan ta hade da jami’an ta a wajen masu wankin Mota na 15-15 Auto Spar Car wash.
Ya yinda a bangare daya , mai horar da tawagar ‘yan wasan Badminton ya yi Alkawarin biyan kudin masauki ga ‘yan wasan dake karkashin sa don kaucewa fadawa halin da sauran ‘yan wasa daban-daban suka shiga na rashin tabbas akan masauki da gararamba a sararin Jami’ar ta Ilorin.
You must be logged in to post a comment Login