Connect with us

Labarai

Wasu bata gari sun kai wa ‘yan sintiri na Vigilante hari a Kano

Published

on

A baya bayan nan ne kungiyar ‘yan sintiri ta Vigilante tare da hadin gwiwar ‘yan sanda, suka gudanar da wani sumame a unguwar Kurna domin magance matsalolin sace-sacen da ya addabi Unguwar, inda suka cafke wasu batagari da dama.

Sai dai da asubahin ranar lahadi da ta gabata ne gun-gun wasu da ake zargin abokan batagarin ne su ka kaiwa ofishin ‘yan Sintirin unguwar Kurna hari tare da kwashe muhimman kayayyakin da jami’an Sintirin ke amfani dasu.

Sadi Hamisu shine Kwamandan ‘yan Sandan al’umma na yankin kan mayanka Kurna, ya ce, yana kwance da asuba ne sai batagarin suka balla kofa suka shigo.

Salisu Dangote shine shugaban kwamitin ‘yan Sandan al’umma na Kurna Kan mayanka, ya yi karin haske kan yadda lamarin ya abku.

Munyi kokarin jin tabakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta DSP Abdullahi Huruna Kiyawa kan faruwar lamarin, sai dai bamu same shi ba, sai dai da zarar rundunar ta magantu zakujimu da su a cikin labaran mu naga ba.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa, batagarin dai sun kaiwa ofishin ‘yan Sintirin hari ne da wasu daga cikin shagunan mutane, bay a ga sace wayoyi da gwala – gwalai da su ka yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!