Kasuwanci
Wasu Direbobi sun zargi jami’an KAROTA da takura musu

Wasu daga cikin shugabannin kungiyar Direbobin motocin Bus, sun koka kan yadda suka ce jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA na yawan tare Membobinsu a kan Titi
Jagoran ayarin Kungiyar Direbobin motocin Busdin dake Garin Kunya a Karamar Hukumar Minjibir, wanda kuma shene sakataren kungiyar Malam Mumfadalu Bukar ya ce yanzu haka direbobin adaidaita sahu sun kwace musu fasinjoji amma hakan baisa sun kokaba.
Ya kuma roki hukumar ta Karota data dagawa Direbobin nasu kafa kamar yadda gwamnati ta dagawa matuka baburan adaidaita sahu.
A jawabin sa, Shugaban hukumar ta KAROTA, Faisal Mahmud Kabir da Daraktan kula da harkokin Kudaden shiga na hukumar Alhaji Nura Ahmad Diso ya ce, abinda direbobin suka kawo koke akan sa hurumi ne na gwamnatin Tarayya, don haka ya shawar ce su dasu miƙa Koken zuwa Hukumar tattara Kudaden Haraji ta Jahar Kano don magan ce al’amarin.
Mai magana da yawun hukumar ta Karota Abubakar Ibrahim Sharada ne ya bayyana yadda wannan zama ya kasance ta cikin wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radio.
You must be logged in to post a comment Login