Connect with us

Labaran Kano

Wasu ‘yan ta’adda sun kai mummunan hari a jihar Katsina

Published

on

Rahotanni daga Jihar Katsina na nuni da cewa ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Doma, da ke Tafoki Ward a Ƙaramar Hukumar Faskari, inda suka kashe mutane da dama.


An ce harin ya faru ne da rana tsaka, inda maharan suka shafe sa’o’i suna barin wuta kafin su janye da misalin ƙarfe huɗu na yamma. Yayin da harin ya yi sanadiyyar konewar wasu gidaje a yankin

Shugaban yankin, Alhaji Surajo Aliyu-Daudawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai bayyana harin a matsayin ramuwar gayya, kuma mafi muni cikin watanni biyar da suka gabata, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka taɓa cimmawa da ‘yan bindigar.

Sai dai rundunar ‘yan sanda ta ce mutane 13 ne suka mutu, inda ta bayyana cewa jami’anta tare da sojoji sun kai ɗauki, amma maharan sun tsere kafin isowarsu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!