Labarai
Wata gobara ta lakume kadarorin miliyoyin kudi a sharkwatar ‘yan Sandan Jihar Kano
Gobara data tashi a sharkwatar rundunar yan sanda ta Bompai, karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano ta yi sanadiyar lakume kadarorin miliyoyin nairori.
Wani shaidan gani da ido ya shaidawa Freedom Radio cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 2 na ranar Asabar, wanda yace ‘ ta shafi ofishin Provost har zuwa ofishin mataimakin kwamishinan yan sanda’.
Ya kuma kara da cewa bayan hakan ne ta bazu zuwa sashin kudi da dakin taro da ofishin Mai magana da yawun Rundunar yan sanda da ofishin mai tallafawa kwamishina a bangaren mulki sai kuma ofishin mataimakin kwamishina da wasu wuraren’.
Sai dai kuma rahoton ya nuna cewa gobarar ba ta shafi sabon ofishin kwamishinan yan sanda da wasu gine-gine da ke kallon ofishin ba.
Ana kyautata zaton cewa gobarar ta kona takardu da dama, amma babu asarar rai, ko kuma rauni a sakamakon gobarar.
Sai dai har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton ba’a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ba.
A hannu guda kuma jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun samu nasarar kashe wutan daga bisani.
You must be logged in to post a comment Login