Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

‘Yan rawar banjo sun tilastawa makarantar islamiyya tashi daga karatu

Published

on

‘Yan rawar banjo sun tilastawa makarantar islamiyya tashi daga karatu

Al’ummar unguwar Dandishe Gabas dake karamar hukumar Dala a nan Kano sun koka kan wata budurwa da suka ce ta addabe su a yankin.

Mutanen unguwar na zargin wata budurwa mai suna Maryam Muhammad mazauniyar unguwar da yawan hada rawar banjo da Casu da kuma DJ, ba tare da wani dalili ba.

Irin hakan ce ta faru a litinin din da ta gabata, inda Maryam ta hada casu ana rakashewa wanda ya tilastawa makarantar islamiyyar dakatar da karatu.

Wakilin mu Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito mana cewa wasu daga malaman makarantar sun nemi tattaunawa da matashiyar don ganin an samar da maslaha sai dai hakan bai yiwu ba, inda ta dallawa daya daga cikin malaman makarantar mari.

Freedom Radio ta yi kokarin jin ta bakin wadda ake zargin amma abin ya ci tura.

Al’ummar yankin dai na fatan ganin mahukunta sun shiga lamarin domin kawo dai-daito.

Rubutu masu nasaba:

An gano wanda ya fito a bidiyon da ake zargin Daurawa ne

Zaurawa sun yi bore kan hana zancen dare a Kano

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!