Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wata Sabuwa: Kamfanin NNPC ya musanta karin farashin mai

Published

on

Kamfanin mai na kasa (NNPC) ya musanta batun karin farashin litar man fetur da hukumar kayyade farashin mai ta kasa (PPPRA) ta sanar a daren alhamis.

A cikin wani sako da kamfanin na NNPC ya fitar a shafinsa na twitter a yau juma’a, kamfanin NNPC ya ce har yanzu farashin mai ya na nan kamar yadda ya ke a baya.

Sakon na NNPC ya jaddada cewa ba za ayi karin farashin mai a watan Maris ba.

Wannan sako na NNPC ya sha bamban da sanarwar da tun farko hukumar kayyade farashin mai ta kasa (PPPRA) ta fitar.

Tun farko dai hukumar kayyade farashin mai ta kasa (PPPRA) ta sanar da cewa yanzu farashin mai ya kai naira dari biyu da goma sha biyu da kwabo sittin da daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!