Connect with us

Labaran Wasanni

WTA : Naomi Osaka ce ta 9 a duniya a kwallon Tennis

Published

on

‘Yar wasan kwallon Tennis, Naomi Osaka ta zama ta Tara a cikin jerin jaddawalin ‘yan wasan kwallon Tennis na mata.

Hukumar wasan kwallon Tennis ta mata WTA, ita ce ta sanar da hakan a yau Litinin, yayin da ‘yar wasan ke tunkarar wasan ta a gasar US Open bayan ta fice daga wasan karshe a gasar Western & Southern Open.

Osaka dai ta gaza fafata wasan karshe a gasar ta Western & Southern Open sakamakon rauni da ta samu, lamarin da ya bai wa abokiyar karawarta, Victoria Azarenka wadda ke rika da lamba 27 a duniya.

Yayin da Ashleigh Barty ta zo ta daya sai Simona Halep a matsayi ta 2 sai Karolina Pliskova ta 3, sai Sofia Kenin ta 4 sai kuma Elina Svitolina ta 5.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,226 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!