Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

UEFA : Ta fitar da jadawalin shiga gasar Champions League

Published

on

Hukumar kwallon kafar turai UEFA ta fitar da jaddawalin zagaye na uku a wasannin neman tikitin gasar Champions League ta kakar wasanni mai zuwa.

UEFA ta fitar da jaddawalin ne daga shalkwatar ta dake kasar Swizerland a yau Litinin.

Yayin da Ferencvaros ta kasar Hungary za ta hadu da Dinamo Zagreb ta kasar Crotia sai Qarabag ta kasar Azerbaijan da za ta fafata da Molde ta kasar Norway, Omonia Nicosia ta kasar Cyprus za ta kara da Red Star Belgrade ta kasar Serbia inda Midtjylland ta kasar Denmark wacce za ta kece raini da Young Boys ta kasar Switzerland.

Sai kuma Maccabi Tel-Aviv ta kasar Isra’ila inda za ta fafata da Dinamo Brest ta kasar Belarus yayin da PAOK ta kasar Girka da Benfica ta kasar Portugal, Dynamo Kiev ta kasar Ukrain da za ta kara da AZ Alkmaar ta kasar Netherlands sai kuma Gent ta kasar Belarus wadda za ta zage damtse da Rapid Vienna ta kasar Australia.

Za dai a fara buga wasanni na siri daya kwale a ranar 15 ko 16 ga wata Satumba mai kamawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!