Labarai
Ya kamata a baiwa mahajjata damar ciyar da kansu-Gagaci
Dagacin Garin Dan Hassan dake yankin karamar hukumar Kura a nan Kano Alhaji Adda’u Sani ya shawarci hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON data baiwa Alhazan bana dama kowa ya ciyarda kansa a lokacin gudanarda ibadar aikin Hajjin bana sakamakon matsalar da ake yawan samu ta abinci a kasa mai tsarki.
Alhaji Adda’u Sani ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da manema labarai.
A cewarsa “Alhazai suna biyan kudin abinci mai yawa, amma sai ka iske ana baiwa Alhazan abincin da bashi suke bukata ba, amma idan aka baiwa kowa dama ya ciyarda kansa za’a magance duk wata matsalar abinci a tsakanin Alhazan Najeriya”.
Freedom Radio ta ruwaito Dagacin Garin na Dan Hassan Alhaji Adda’u Sani ya koka kan yadda a bana aka samu matsalar tashin farashin kudin kujerar aikin Hajjin bana da hakan ke nuna cewa duk Alhajin da yake bukatar zuwa aikin Hajji a wannan shekarar wajibi ne ya biya naira miliyan hudu da dubu dari biyar a matsayin kudin farko.
Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
You must be logged in to post a comment Login