Kiwon Lafiya
Ya kamata a rika tallafa wa masu ciwon Koda- Sarkin Hadejia

Mai Martaba Sarkin Hadejia kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar Jigawa Alhaji Adamu Abubakar Maje, ya ce, ya kamata al’umma da kuma kungiyoyi su mayar da hankali wajen tallafa wa mutanen da ke fama da ciwon Koda domin rage musu radadin halin da suke ciki sakamakon tsadar rayuwa da kuma irin kudaden da masu fama da lalurar ke kashewa.
Sarkin ya bayyana hakan ne a Alhamis din makon nan, lokacin da Gidauniyar tallafa wa masu fama da ciwon Koda ta Kidney Care Foundation ta mika tallafin kayayyakin aikin wankin koda da kudin su ya haura Naira miliyan daya da rabi ga masarautar Hadeja.
Sarkin ya kuma kara da cewar masarautar ta Hadejia na kan gaba wajen yawan mutanen da ke fama da ciwon Koda, don haka tallafin zai taimaka wajen saukaka wa wadanda ke fama da cutar.
You must be logged in to post a comment Login