Labarai
Ya kamata gwamnati ta habaka abubuwan more rayuwa ga masu bukata ta musamman: Aisha Lawan Saji
Ma’aikatar harkokin mata da kananan yara da matasa da kuma kula da al’amuran mutane masu bukata ta musamman ta jihar Kano, ta bukaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta gaggauta samar da karin asibitin kula da mutane masu bukata ta musamman tare da samar musu karin makarantu da kuma wuraren koyon sana’o’in dogaro da kai.
Kwamishinar ma’aikatar Hajiya Aisah Lawan Saji Rano, ce ta bukaci hakan yayin da kwamitin majalisar dokokin Kano mai lura da al’amuran ma’aikatar ya kai mata ziyarar aiki da safiyar yau Juma’a.
Shugaban ma’aikatar ta kuma ce, ‘akwai bukatar gwamnatin ta mayar da hankali wajen tallafa wa mata da matasan jihar Kano musamman la’akari da irin halin da ake ciki a yanzu na tsananin rayuwa’.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin majalisar mai kula da ma’aikatar Ahmad Muhammad Tomas wakilin Makoda da ya samu wakilcin mataimakinsa Abubakar Danladi Isah mai wakiltar Gaya, ya bayyana makasudin ziyarar tare da bayar da tabbacin goyon baya ga ma’aikatar.
Freedom Radio ta ruwaito cewa, Hajiya Aisha Lawan Saji Rano, ta kuma bayyana cewa, yanzu haka wuraren da dama da ke karkashin ma’aikatar sun samu gagarumin sauyi musamman gidajen marayu da suka samu sauyin cimaka da wasu sauran aikace-aikace.
RAhoton:Auwal Hassan Fagge
You must be logged in to post a comment Login