Labarai
Ya kamata likitocin asibitin kashi na Dala su rage kudade ga marasa lafiya: Sarkin Kano
Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya tunatar da asabitin kashi na dala kan su kula da tsarin ayyukansu wajen tausayawa marasa lafiya, ta hanyoyin rage musu kudaden magani a asibitin, don ragewa al’umma radadin da suke ciki.
Sarkin yayi wannan kira ne lokacin da ma’aikatan asibitin kashi na dala karkashin jagorancin sabon shugaban asibitin Dakta Nuraddeen isah suka ziyarce shi a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace, “duba da yanda al’umma suka samu kai a ciki na rashin kudi da sauran wahalalu ya kamata suyi duba da hakan wajen rage kudin magani a asibitin”.
A nasa jawabin Sabon shugaban asibitin Dakta Nuraddeen Isah ya tabbatarwa da sarkin cewa, “zasu fidda sabon tsarin da zai taimakawa marasa lafiya, tare kuma da yin amfani da motocin da asibitin ya samar don dauko marasa lafiya”.
Freedom Radio ta rawaito cewa Sabon shugaban asibitin kashi na dala yace ‘sun horar da likitoci daban-daban don kula da lafiyar al’umma da kuma magance fita kasashen ketare don neman lafiya’.
Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login