Labarai
Ya kamata NAHON ta sake duba farashin canjin kudade don rage tsadar kujerun Hajji: Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bukaci hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON da ta sake duba farashin canjin kudadenta domin samar da sauki a aikin hajjin da za a yi nan gaba.
Shettima ya mika bukatar ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin hukumar ta NAHCON karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Zikrullah Hassan a fadar shugaban kasa da ke Abuja jiya Laraba.
Shettima ya kuma shawarci hukumar ta NAHCON da ta yi duk shirye-shiryen da ake bukata don bawa alhazai kulawar da suke bukata.
Kasheem Shettima ya kara da cewa la’akhari da aikin Hajji aikin ibada ne, bai kamata hukumar ta yi wasarere da walwalar mahajjatan ba tsawon zamansu a kasa mai tsarki ba.
Rahoton: Yusuf Sulaiman
You must be logged in to post a comment Login