Kiwon Lafiya
Ya na da kyau mutane su san illar cizon mahaukacin kare- Mafarauta
Shugaban mafarauta ta zaman lafiya a Kano Sani Muhammad Gwangwazo ya ce wayarwa da mutane kai dangane da cizon mahaukacin kare a cikin al’umna’ abune Mai mahimmanci sosai, duba da rashin sanin ilar da cizon Karen take da shi a cikin al’umna’.
Alh Sani Muhammad Gwangwazo ya bayyana hakan ne yayi Taron da ta kungiyar likitocin dabbobi ta Ƙasa reshen Jihar Kano ta shirya da yardar Shirin FCDO, da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya data gona a Jihar kano, kan ranar cizon kare ta duniya na shekarar 2023, da majalisar Dinkin duniya ta ware ranar.
Wanda ya ce ‘wannan taron wayar da kan kamar don mafarautan akayi shi, duba da cewa sunfi kowa mu’amala da karnuka, wanda taron zai taimaka musu wajen sanin yanda zasu mu’amalanci karnuka nasu, har ma da kiwonsu’.
A nasa bangaren kwamishinan gona na Jihar Kano, ta bakin mai bashi shawara na musamman Rabi’u Salisu Baffa cewa yayi, ‘gwamnati a shirye take wajen ganin ta tallafawa wannan kungiyar, za Kuma su duba Wani bangare ne ya kamata ta Bada tallafi ta bayar, inda zata Bada shawara ta bayar, da sauran duk abinda ya kamata’.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun bayyana cewa sun karu matuka, musamman ma kan lokutan faya kamata rinka yiwa karnuka allura rigakafi, da kuma illolin da cizon karen yake yiwa al’umna’.
You must be logged in to post a comment Login