Connect with us

Labarai

Yadda ɗan China ya hallaka Ummita a Kano

Published

on

Hukumomi a Kano sun cafke wani ɗan ƙasar China mai suna Mr Geng bisa zargin hallata wata mata Ummukulsum Buhari da aka fi sani da Ummita a unguwar Janbulo.

Rahotonni sun ce, Mr. Geng wanda tsohon saurayin Ummulkhairi ne ya kutsa kai cikin gidansu a daren Jumu’a, inda ya caka mata wuƙa.

An garzaya da ita asibitin UMC da ke Janbulo, a nan ne kuma rai yayi halinsa.

Wani makusancin marigayiyar ya ce, sun shafe kusan shekaru biyu suna soyayya da Mr Geng kafin ta yi aure da wani.

Sai dai daga bisani auren nata ya mutu, amma shi Mr Geng bai daina bibiyarta ba.

Tuni dai jami’an hukumar shige da fice ta ƙasa suka cafke Mr Geng tare da miƙa shi ga ƴan sanda domin ci gaba da bincike.

Freedom Radio ta so jin ta bakin mahaifiyar Ummita amma bata amince ta yi magana ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!