Labarai
Yadda aka gudanar da jana’izan marigayi Iyan Zazzau a Zariya
Babban limamin Zazzau Shaikh Dalhatu Kasim Imam ya jagoranci jana’izar Marigayi Iyan Zazzau Alhaji Bashir Aminu, ya yin da Shaikh Sani Khalifa ya gudanar da addu´a ta musamman ga marigayin.
An dai gudanar da jana´izan marigayin ne da misalin karfe goma na safe a babban masallacin juma´a na kwata da ke Sabon gari inda aka binne shi a gidansa dake GRA Sabo garin Zariya.
Janaizar ta sami halartar manyan mutane ciki har da ministan sufirin jiragen sama Dr. Hadi Sirika inda ya bukaci ‘yan uwa da abokanan arziki da su cigaba da yi mishi addu´o´i.
Kogunan Zazzau Alhaji Abdulkareem Bashar Aminu Babban da ne ga marigayin ya bayyana mahaifin nasu a matsayin mutum mai son Zaman lafiya na al’umma
Marigayin ya taba zama hakimin Sabon gari daga shekara 1979 zuwa 2018 kuma ya fito daga gidan sarauta na katsinawa.
Yana daga cikin wadanda suka nemi kujeran sarauta na masarautar zazzau bayan rasuwar Sarkin Zazzau na 18 Dr. Shehu Idris a watan Satumba na shekarar da ta gabata.
Marigayin Alhaji Bashir Aminu ya rasu ne da safiyar ranar juma´a yana da shekaru 70 ya bar mata 4 da ya ya 32.
Wakilin Freedom Radio Hassan Ibrahim ya rawaito cewa Marigayi Talban Zazzau Hakimin Igabi Alhaji Abdulkadir Iya fate na daya daga cikin manyan sarautu na gidan mallawa wanda ya rasu jiya an riga anyi janaizar shi kamar yanda addinin musulunci ya shimfida
You must be logged in to post a comment Login