Connect with us

Labarai

‘Yan sanda sun cafke wani gawurtaccen ‘dan daba a Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta cafke wani fitaccen dan sara suka mai suna Aminu A. Aminu dan shekaru 21 wanda ake zargi da addabar al’ummar unguwannin Sagagi da Kwalli a karamar hukumar birnin Kano.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaidawa Freedom Radio cewa sun samu korafi daga wani mai suna Mubarak Abdul dan shekaru 31 mazaunin unguwar Sagagi wanda yayi korafin cewar Aminu A. Aminu ya daba masa wuka a wuya.

DSP. Kiyawa ya ce, tuni suka garzaya da wanda aka yiwa raunin zuwa asibitin Murtala sannan, suna ci gaba da bincike akan lamarin domin gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!