Labarai
CP Singham ya musanta zargin ya rasu
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2021/02/107C1544-3EB7-48F9-9527-AA1B006DA750.jpeg)
Tsohon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Muhammad Wakili ya musanta zargin da ake yadawa cewa ya rasu.
CP Muhammad Wakili mai ritaya ya bayyana hakan ne a tattaunawar sa da wakilin mu Hassan Muhammad Auwal a gidan sa dake jihar Gombe.
Tsohon kwamishinan yada labarai ya ce labarin bai bashi mamaki ba kasancewar masoya sun ta tuntubar sa.
Tun a jiya ne wasu kafafan sada zumunta suke yadawa cewa, tsohon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Muhammad Wakili ya rasu.
An ta yi ta yada jita-jitan cewa Tsohon kwamishinan ‘yan sandan wanda aka fi sani da Singham ya rasu a wani mumunan hadarin mota da ya afko.
Akan haka ne mutane suka yi ta bayyana alhinin su da jimami kan rasuwar ta sa a kafafan sada zumunta.
You must be logged in to post a comment Login