Connect with us

Labarai

Yadda guda daga cikin manyan kwamandojin kungiyar boko Haram ya mika wuya

Published

on

Shalkwatar tsaron kasar nan tace wani guda daga cikin manyan kwamandojin kungiyar boko Haram ya mika kansa ga shalkwatar tasu tare da matansa guda hudu bayan wata karan batta da sukayi da jami’an sojin a tsakanin sha bakwai ga watan da muke ciki zuwa Ashirin da uku ga watan na Satumba.

Mai Magana da yawun rundunar Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana hakan a wani taron karshen mako-mako da rundunar take gudanarwa a birnin tarayya Abuja.

Manjo John Enanche ya kuma ce nasarar da suka samu ta biyo bayan wata musayar wuta da aka yi tsakanin dakarun Operation Lafiya Dole da ‘yan tada kayar bayan a Jihohin Borno da Taraba da kuma Adamawa.

Ya kuma ce a Borno sun yi nasarar kama mutum guda a karamar hukumar Kamuya a karamar hukumar Biu a jihar Borno yayin da sauran mutane Tara aka kama su ne a karamar hukumar Wukari dake jihar Taraba.

Manjo Janar John Enanche ya kuma ce a yayin musayar wutar rundunar tayi nasarar kwato wasu motoci da sauran kayayyakin da suke ta’addanci da su

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!