Kimiyya
Yadda iPhone 11 ta yamutsa hazo a soshiyal midiya
Yadda iPhone 11 ta yamutsa hazo a soshiyal midiya
A ranar 10 ga watan Satumban da muke ciki ne kamfanin sarrafa na’urorin sadarwa na zamani wato Apple ya kaddamar da sabbin kayayyaki, ciki harda wayoyin iPhone 11, iPhone II Pro da kuma Pro Max, wato dai zafafan wayoyi guda uku daga kamfanin.
Wadannan wayoyi dai sun kunshi wasu abubuwa na musamman wadanda suka yiwa sauran wayoyi zarra, an gina kwakwalwar iPhone 11 akan A13 Bionic, a bangaren karfin ma’ajiyar bayanai kuwa wato Memory ta fara daga 64GB, 256GB, da kuma 512GB.
A bangaren kyamara (camera) kuwa iPhone 11 tana da girman 12PM + 12PM, baki dayan kyamarar wayar kuwa iPhone 11 tazo da kyamara guda biyu (2) yayin da iPhone 11 Pro da Pro Max suka zo da kyamara guda uku, wadannan wayoyi dai sune kan gaba wajen karfin kyamara a halin yanzu a duniya.
Game da girman jikin kuwa wayoyin sun kai inci 5.94 x 2.98 x 0.33, babu maganar rashin rike caji domin kuwa an yiwa wadannan wayoyi kyaky-kyawan shiri wajen rike caji na tsawon lokaci.
Akwai wayoyin iPhone 11 kaloli da dama wadanda suka hadar da Fara, Baka, Ruwan Dorawa, Koriya, Ja da kuma Ruwan Hoda.
A ranar 20 ga watan Satumban da muke ciki ne dai aka fara sayar da iPhone 11 akan kudi dalar Amurka $3600 wanda ya kama N252, 000 a kudin mu na nan gida Najeriya.
An kafa kamfanin Apple ne a watan Afrilu na shekarar 1987, a birnin California na kasar Amurka, a yanzu dai yana daya daga cikin manyan kamfanonin kere-keren fasahar zamani dake jan zare a duniya.
A nan gida Najeriya wayar iPhone ta zamo wata abar alfahari ga al’umma, musamman matasa wanda kowa ke ribibi wajen ganin ya mallaki waya kirar kamfanin, hakan ne ya sanya labarin kaddamar da iPhone 11 ya zamo jigon tattaunawa a shafukan sada zumunta, inda matasa suka dinga wallafa bayanai kala-kala akan wannan wayar, hakan yasa muka leka dandalin sada zumunta na Twitter da kuma Facebook inda muka dauko muku wasa daga tattaunawar da matasan keyi.
Not the best comparison but here’s the iPhone 8 Plus vs iPhone 11 Pro Max (with night mode on) pic.twitter.com/WCxs0cMelj
— Joel Franco (@OfficialJoelF) September 21, 2019
#IPhone 11 tafara raba xumunci na old friends tana connecting na new friendships..! Alamu sun nuna anfara daidaita sahu a kasar nan kwarya tabi kwarya
— Saleeth G Garba (@Dan_yayan_kano) September 23, 2019
Yan Nigeria aita complain Qasa ba kudi amma sabon waya na fitowa sune sahun gaba duk tsadan ta. Allah yasa Mudace https://t.co/ScH8tDZ3Qr
— MUSBEY (@Mus6ey) September 20, 2019
First Pic: iPhone X Cases -N2000 each
Second and Third Pic: iPhone X Tempered Glass Cases -N2500 each
Fourth Pic: iPhone 7/8 Plus Silicon Hijab and Melanin Case -N2000 eachRT please, my customer might be on your timeline. ??❤️ pic.twitter.com/aelbLl1K1C
— Balkisa Naira (@Bilkyysu) September 7, 2019
Ku bayyana mana ra’ayoyin ku dangane da iPhone 11.
Basheer Sharfadi
23rd, September, 2019.