Labarai
Yadda kafofin sada zumunta ke ingiza matasa tsallakawa kasashen waje – IOM
Hukumar kula da masu kaura ta duniya IOM ta ce kafofin sada zumunta na zamani ne ke ingiza matasan kasar nan wajen ganin sun tsallaka kasashen waje domin samun rayuwa mai inganci.
Babban jami’in hukumar a Najeriya Mr Frantz Celestin ya bayyana hakan yayin taron manema labarai game da rawar da kaurar jama’a ke takawa kan kalubalen tsaro a duniya.
Ya ma buga misali da ‘yan Najeriyar da suka dawo daga kasar Libya, wadanda mafi aksarinsu sun fito ne daga Jihohin kudancin kasar nan.
Mr Celestin ya ce labaran da ake wallafawa a shafukan sada zumunta na zamani kan irin daular da ake shiga a kasashen waje musamman Turai ne ke tunzura matasan har su sanya burin zuwa can.
Ya kara da cewa duk da malolin tsaron da ake fuskanta a yankin arewa maso gabashin kasar nan a shekarun nan, kididdiga ta nuna cewa hakan bai sanya matasa masu yawa sun yi kwadayin ketarawa kasashen wajen ba.
Jihohin da aka fi samun matasa masu haurawa kasashen waje daga kasar nan sun hadar da Edo da Delta da Lagos da Imo da kuma Ogun.
You must be logged in to post a comment Login