Labarai
Yadda Magunguna Ke Bacewa Tsakanin Kasafin Kuɗi da Cibiyoyin Lafiya a Kano

Duk da ƙaruwar kuɗaɗe da ake warewa domin Asusun Samar da Kula da Lafiya na Asali watau Basic Health Care Provision Fund (BHCPF) a Najeriya, cibiyoyin lafiya na matakin farko watau PHC da dama a Jihar Kano har yanzu na fama da ƙarancin magunguna da kayan aiki, lamarin da ke tilasta wa marasa lafiya sayen magani daga aljihunsu.
A Cibiyar Lafiya ta Tsohuwar Rogo da ke Karamar Hukumar Rogo, akwatunan magunguna sun kusan zama fanko. Ƙananan magunguna kaɗan ne kawai ake samu, yayin da babu yawancin muhimman magunguna da ya kamata ana samu.
Khadija Auwal, uwa mai ‘ya’ya uku, ta ce ta saba komawa gida da takardar sayen magani maimakon maganin. “matsalar nan tana sosa mana rai sosai mu rika sayen magunguna a waje, alhali gwamnati ta ce an tanadar mana su,” in ji ta. Wani lokaci kuma tana amfani da ganyayyaki idan ba ta da kuɗin sayen cikakken magani.
Haka zalika, Maryam Musa, mai juna biyu, ta ce ta sayar da akuya domin sayen maganin zazzabin cizon sauro bayan da babu shi a cibiyar lafiya. “Rayuwa ta da ta jaririna ce ta sa na yanke wannan shawara,” in ji ta.
A cewar Hukumar Kula da Lafiya ta Ƙasa (NPHCDA), ya kamata kowace cibiyar lafiya ta mallaki sashen magunguna da dakunan jinya da ruwa da wutar lantarki da kuma sauran muhimman kayan aiki. Sai dai bincike ya nuna cewa da dama daga cikin cibiyoyin lafiya a Kano ba su cika waɗannan ka’idoji ba.
Wasu shugabannin al’umma da kwamitocin kula da lafiya sun ce duk da ana turo kuɗaɗe zuwa cibiyoyin, ba sa wadatarwa, sannan sau da dama ana sakin su ne a makare. Wasu ma’aikatan lafiya kuma sun yi zargin raunin sa ido da rashin gaskiya wajen kashe kuɗaɗen.
A Yandadi dake Karamar Hukumar Kunchi, bayanai a rubuce sun nuna an fitar da sama da naira dubu dari huɗu domin sayen magunguna, amma abin da aka gani a cibiyar bai dace da wannan adadi ba, lamarin da ya haifar da tambayoyi kan inda kuɗin suka shiga.
Duk da cewa Jihar Kano na ware biliyoyin naira a kasafin kuɗinta domin harkokin lafiya, rahotanni sun nuna cewa kashi kaɗan ne ake kashewa a aikace, abin da ke barin cibiyoyin lafiya cikin ƙunci.
Masana sun ce matsalar ba rashin kuɗi ba ce, illa dai yadda ake sarrafa su bayan an sake su. Sun jaddada bukatar ƙarfafa sa ido, gaskiya, da shigar da al’umma cikin bin diddigin kuɗaɗen.
Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko ta Jihar Kano ta amince da cewa ana ware kuɗaɗe ga cibiyoyin, amma jinkirin sakin kuɗin na kawo cikas ga ayyuka.
Har yanzu, buƙatar neman bayanai karkashin dokar ‘Yancin Samun Bayanai (FOI) da aka aikewa Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano kan yadda ake kashe kuɗaɗen BHCPF ba ta samu amsa ba.
A halin yanzu dai, al’ummomin karkara na ci gaba da biyan kuɗin magungunan duk da kudaden da gwamnati taka tanadarwa domin su, yayin da tambayoyi ke ƙara yawa kan gaskiya da amincin tafiyar da kuɗaɗen lafiya a jihar.
Wannan rahoton ya samu ne bisa goyon bayan Cibiyar Ƙasa da Ƙasa ta Rahotannin Binciken Kwakwaf (ICIR), a ƙarƙashin shirin Strengthening Public Accountability for Results and Knowledge (SPARK 2.2), wanda ke da nufin ƙarfafa gaskiya da sa ido da kuma amincin amfani da kuɗaɗen gwamnati, musamman a ɓangaren lafiya.
You must be logged in to post a comment Login