Labarai
Yadda Majalisa ta nemi minista da manyan hafsoshin Najeriya su gurfana a gabanta
Majalisar dattijai ta gayyaci ministan tsaro da manyan hafsoshin tsaron kasar nan da su gurfana gabanta don yin karin haske game da tabarbarewar harkokin tsaro a kasar nan.
Sauran wadanda majalisar ta gayyata sun hada da: sufeto janar na ‘yan sandan kasar nan Muhammad Adamu da shugaban hukumar tsaron sirri ta DSS Yusuf Magaji Bichi.
Majalisar ta dau wannan mataki ne biyo bayan kudirin gaggawa da sanata mai wakiltar mazabar Katsina ta kudu, Bello Mandiya ya gabatar.
Da yak e gabatar da korafi yayin zaman majalisar nay au, sanata Bello Mandiya ya ce wajibi ne ministan tsaro da manyan hafsoshin tsaron su gurfana musamman idan aka yi la’akari da sace daliban makarantar sakandiren jihar Katsina.
You must be logged in to post a comment Login