Labarai
Yadda masu yin Gurasa suka yi Zanga-zanga a Kano
Kungiyar mata masu yin gurasa a jihar kano ta bayyana cewa tsadar da Fulawa ta yi ya tisalta musu dole su dakatar da Aikin su har sai abun da hali yayi ko kuma idan Mahukunta sun shiga cikin maganar.
” Tsadar fulawar da muke aiki da ita ta yi yawa, kullum muka je siya sai anyi mana karin akalla Naira dubu daya da dari biyar , yanzu maganar da nake yi muku muna siyan Fulawa sama da Naira dubu 40 to ya zamu yi”.
Shugabar kungiyar masu yin gurasa ta jihar kano Fatima Auwal Chediyar yan gurasa ce ta bayyana hakan yayin wata zanga-zangar lumana da suka gudanar a a safiyar yau juma’a.
” Muna gudanar da wannan zanga-zangar ne domin mu nunawa shugabannin mu halin da muke ciki, kuma kasuwancinmu na talakawa ne saboda idan suka ga yadda muke Sana’ar wallahi ba za su iya ba, Muna cikin masifa fulawar da muke aiki da ita tafi karfinmu”.
Fatima Auwal ta bukaci shugabannin a matakai daban-daban da su dubi halin da suke cikin na tsadar fulawa su taimaka musu saboda yawa ‘ya’yan da suke da su, ga shi kuma da wannan Sana’ar suka dogara wajen ciyar da ya’yan da kuma biya musu kudin makaranta.
Matan dai sun ce dole su hakura da yin gurasar saboda basu da jarin da zasu sayi fulawar, kuma yin hakan wata babbar barazana ce ga al’umma musamman masu karamin karfi wadanda ba sa iya siyan biredi.
You must be logged in to post a comment Login