Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya nemi bangarori masu zaman kan su, su dauke matasa ayyukan yi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi  bangarori masu zaman kan su dake jihohi 36 na kasar nan da su dauki matasa ayyukan yi a hukumomin su  har da ma babban birnin tarayya Abuja.

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a birnin Abakaliki ya yin kaddamar da shirin samarwar matasa ayyukan yi  dubu 774 a hukumomin kasar nan na (ESPWP) .

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Shugaban kasar wanda ya sami wakilcin ministan kimiya da fasaha Dr, Ogbonnaya Onu.

Ministan ya yi bayanin cewa, an kirkiro da shirin ne don rage radadin Annobar cutar corona da ta durkusar da tattalin arzikin kasa da na mutane da kuma yadda aka gudanar da rikicin zanga-zangar #EndSARS.

Tun da fari, shugaban shirin a jihar Ebonyi Dr, Edward Nkwegu ya ce gwamnatin tarayya zata kashe fiye da Naira Miliyan 7 a cikin watannin 3 farko a jihar ta Ebonyi ita kadai.

Shirin dai zai maida hankali ne wajen daukar mutum dubu 1000 a kowacce karamar hukuma ya yin da za’a biya kowanne mutum daya Naira dubu 20 a watannin 3.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!