Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda na kuɓuta a harin jirgin ƙasa – Rahma Abdulmajid

Published

on

Wata mata da ta kubuta daga harin jirgin kasa a ranar Alhamis a hanyar Abuja zuwa Kaduna ta ce, ƴan bindiga ne sun kai hari a jirgin nasu.

Rahma Abdulmajid Sharif ta bayyana hakan ga freedom radiyo jim kaɗan bayan data kubuta da harin da aka kaiwa jirgin kasa a yammacin Alhamis

“muna cikin jirgin ne sai muka ji wata ƙara mai karfi alamun abu ya fashe sai fitulu da komai na jirgin ya dauke”.

“A lokacin babu network da za a kira mu a fada mana abinda ke faruwa sai muka ga wani jirgi ya taho mu kuma ba damar mu koma kasancewar hanya ɗaya ce”

Ta ci gaba da cewa “anan aka ajiye mu inda jirgin ya tsaya babu ruwa babu kuma jami’an tsaro ba kuma wanda zai faɗa mana abinda ke faruwa har sai bayan awa uku aka sa sabon kan jirgi muka wuce Abuja”.

Rahma Abdulmajid ta kuma ce “Jirgin da aka fara kaiwa harin ƴan bundiga sun harbe shi daga bisani ya samu tserewa da ƙyar, domin kuwa harbi ya lalata shi babu damar ya ci gaba da amfani”.

“Sai bayan mun zo Abuja muka samu labarin abinda ke faruwa duk da tsahon lokacin da muka shafe a hanya kafin mu iso sakamakon yadda jirgin yayi fatafata kuma hanyar ma ta lalace”.

A ranar Alhamis aka kaiwa jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna hari lamarin da ya sanya hukumar kula da zirga-zirga giragen kasa NRC ta dakatar da cigaba sufurin jiragen a fadin ƙasar nan.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!