ilimi
Yadda wasu ɓata gari suka addabi makarantar Mai Kwatashi da sace-sace

Kwamitin amintattu na ƙungiyar tsofaffin ɗalibai da kuma na al’umma gatan makaranta SBMC na Sakandaren Maza da ta mata na Mai Kwatashi da ke unguwar Sabon Gari a yankin ƙaramar hukumar Fagge, sun bukaci ɗaukin gwamanatin jihar Kano, bisa yadda ɓata gari suka addabi makarantun na Mai Kwatashi ta maza da ta mata da sace-sace.
Shugaban kwamitin amintattu ƙungiyar Mista Ifeanyi Chinweuba ne ya buƙaci hakan yayin ganawarsa da manema labarai ranar Asabar.
Mista Ifeanyi na wannan koke ne biyo bayan yadda ɓata gari suke ɓalle ƙofofi da tagogin Makarantar cikin dare, yayin da wasu lokutan ma har da tsakar rana.
Ya ce, an shafe tsawon shekaru suna fama da wannan ɓarna inda har ta kai a yanzu haka sun kammala cire kusan dukkan wasu kaya masu amfani da ke makarantar.
A nasa ɓangaren, shi ma shugaban Kwamitin SBMC na Makarantar Malam Abdulaziz, ya bayyana yadda makarantar ta Mai Kwatashi ta zama wata babbar maɓoya ga ɓata gari da suke yin amfani da ita wajen cin karensu ba babaka.
Ɓata garin matasan, sun lalata ajujuwa 24 na makarantar da ɗakin gwaje-gwaje har ma da dukkan ofisoshi.
You must be logged in to post a comment Login