Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Rahoto : Yadda ‘yan kasuwa a Kano ke koka kan karyewar jari tun bayan Corona

Published

on

Daga Abdulkareem Muhammad Abdulkareem

Daga lokacin da annobar cutar covid-19 ta bulla a nan Kano ‘yan kasuwa da sauran masu gudanar da sana’oi daban-daban ke cigaba da kokawa musamman ganin irin yadda dokar zaman gida wato Lockdown ya tilasta durkushewar al’amuran kasuwancinsu.

An shafe watanni masu yawa a nan Kano ana fama da zaman gida na kulle kafin gwamnatin Kano ta sanya wasu ranaku domin a fita ayi siyayya lamarin da ya sanya ‘yan kasuwa da dama fara karyar da kayansu domin su sami damar ciyarda iyalansu.

Bayan kwashe tsahon lokaci ana zaman fargaba a nan Kano sakamakon zuwan annobar cutar covid-19 a tsakanin al’umma, al’amura sun tsaya cak kama daga bangaren harkokin kasuwanci da sauran bangarorin da suka shafi Ilimi harma da bangaren zirga-zirga.

Zuwa yanzu dai a Kano ‘yan kasuwa na cigaba da kokawa musamman a wannan lokaci da rashin ciniki, bayaga irin nakasu da jarinsu ya samu saboda corona lamarinda yasanyasu tafka asara mai yawan gaske a cikin harkokinsu na kasuwanci.

Abdullahi Abubakar gudane cikin ‘yan kasuwa a Kano wanda yake fita wasu jihohin kasar nan domin gudanarda kasuwanci wato Bajakoli wanda yanzu yace ya hakura da wannan kewaye sabaoda babu inda ake gudanarda manyan taruka wanda dama sai anyi suke samu.

Gwamnatin Kaduna ta garkame gidajen saida abinci kan take dokar Corona

Rahoto : Yadda tsaftar mahalli na ma’aikatu da kasuwanni ya kasance a Kano

Dattijo Malam Isma’il Muhammad dake sana’ar wankin Hula daya shafe sama da shekaru ashirin da bakwai yana gudanarwa yace yatsinci kansa cikin mawuyacin hali sakamakon annobar covid-19 wanda a yanzu al’amuran sana’arsa ya samu matsala.

“Malam Ismail Muhammad ya kara da cewa bayaga irin yadda farashin kayayyakin amfanin yau da kullum yayi tashin gauran zabi a yanzu, ga kuma matsalar da yake fuskanta na rashin kasuwa wanda hakan yasa ko bako bayaso yayi”.

‘Yan kasuwa dai a nan Kano na cigaba da kira ga gwamnatoci a dukkannin matakai dasu dauki gabarar cigaba da tallafawa irin wadannan ‘yan kasuwa domin tsamosu daga cikin matsanancin halinda suke ciki a yanzu domin kawo musu agaji.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa  ya ce ya lura da matsalolin da wasu daga cikin ‘yan kasuwa suke fuskanta a wannan lokaci dama yadda suka tsinci kansu a lokacin annobar cutar corona virus.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!