Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kaduna ta garkame gidajen saida abinci kan take dokar Corona

Published

on

Ma’aikatar dake kula da harkokin kasuwanci,kirkire-kirkire da fasaha ta jihar Kaduna ta garkame gidajen saida abinci da kayan kwalama da kuma na barasa kuda 6 saboda take dokokin da aka shinfida don kare kai daga kamuwa daga cutar Korona.

An dai rufe gidajen saida abincin da kayan kwalam ne ya yin da ma’aikatar ke zagayen gani da idu don tabbatar ana amfani da dokokin da aka shinfida kan Corona wajen amfani da su a wuraren da ya dace don kare kai daga kamuwa da cutar COVID-19.

Kamfanin dilancin labaru na kasa ya rawaito cewa tawagar kwamishinan ta kai ziyarar ba zata ne  Otel-Otel da gidanjen abinci da shaguna saida kayan kwalama na jihar ta Kaduna

Kwamishinan kasuwanci da fasaha na jihar Kaduna Sama’ila Idris-Nyam ne y sanar da hakan cewa, ayarin ma’aikatar ta ziyarci wuraren kasuwanci goma sha shida ya yin da ta kama 6 daga ciki da laifi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!