Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya fara sayar da kadarorin da aka kwace daga masu cin hanci Najeriya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta fara sayar da kadarorin da gwamnati ta kwace a wajan wasu ‘yan kasar nan da ake zargin su da aikata cin hanci da rashawa.

Shugaban kwamitin sayar da kadarorin Dayo Apata ya bayyana wa manema labarai a Abuja.

Apata yace kadarorin sunkai ashirin da biyar a gurare daban daban a fadin kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da kwamitin a ranar tara ga watan Nuwamba wanda ya umarci ofishin atoni general na kasa domin ya shirya hanyoyin sayar da kadarorin.

Kwamitin ya hada da wakilai daga fadar shugaban kasa da rundunar yan sanda,da hukumar EFCC da kuma da kuma wakilci daga maaikatar kudi,sharia da kuma maikatar ayyuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!