Labarai
Yajin aiki: Daliban jami’a sun fara martani kan zaman gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU
Gwamnatin tarayya ta amince ta cire malaman jami’oin kasar nan daga cikin tsarin albashin na IPPIS tare da biyansu ariya na albashinsu tun daga watan Fabrairu zuwa Yuni.
A bangare guda kuma gwamnatin ta amince ta biya malaman jumillar wasu hakkokinsu da suka hada da alawus da ya kai naira biliyan 65 wanda hakan na daya daga cikin dalilan da suka sanya kungiyar ta tsunduma yajin aiki.
Wannan na zuwa ne bayan zaman da gwamnatin tarayya tayi da kungiyar ASUU a juma’ar nan.
To ko ya ya daliban jamio’i anan Najeriya suka ji ga me da wannan labari?
Wakilinmu Bilal Nasidi Muazu ya tattauna da wasu daga cikin daliban anan Kano, inda suka bayyana cewa” matukar aka dawo makaranta ya zama wajibi malaman su dawo musu da darussa farko domin kuwa sun manta abinda suka koya”
Yayin da wasu ke cewa “An yi tufka da warwara ne kawai a fannin ilimi, domin kuwa da yawanmu baza mu iya tuna a ina aka kwana a darasin da suke karanta ba”
Idan dai za a iya tunawa kimanin watanni 8 kenan ana tsaka da yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login