Labarai
Yajin aiki: majalisar wakilai ta goyi bayan bai wa bangaren shari’a ‘yancin cin gashin kai
Majalisar wakilan Najeriya ta goyi bayan kudirin bai wa bangaren shari’a ‘yancin cin gashin kai, wanda hakan zai bai wa bangaren shari’a damar yin aiki ba tare da tsangwama ba.
Kwamitin majalisar kan harkokin shari’a ya bayyana hakan ne a ganawar sa da mambobin kungiyar ma’aikatan bangaren shari’a ta kasa jiya a Abuja.
Shugaban kwamitin, Onofiok Luke, ya ce majalisar ta goyi bayan su ne, sakamakon yadda bangaren shari’ar ke da matukar muhimmanci ga dorewar dumokradiyya da ayyukan bangarorin gwamnati uku.
A cewar kwamitin majalisar, yana bukatar samun karin bayani daga kungiyar lauyoyin don lalubo hanyoyin magance matsalar su.
You must be logged in to post a comment Login