Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya gamsu a bawa bangaren shari’a damar cin gashin kai

Published

on

Gwamnan jihar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya gamsu da bin tsarin mulkin kasa kan bawa bangaren shari’ar damar cin gashin kanta.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano ta kai masa ziyara don neman amincewarsa tare da yin biyayya ga hukuncin kotu na tabbatar da cin gashin kai ga bangaren na shari’a.

Shugaban kungiyar reshen jihar Kano Aminu Gadanya ya ce “Kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar da cin gashin kai ga bangaren shari’a hakan ya sanya muke kokarin ganin an tabbatar mana da shi.”

Gwamna Ganduje ya kuma ce, akwai tattaunawa da ake tsakanin fannin shari’a da kungiyar gwamnoni ta kasa kuma duk abinda suka yanke a kai ita jihar Kano zata amince da shi.

Haka zalika kungiyar ta mikawa gwamnan takaddar dake bukatar amincewa da cin gashin kan bangaren na shari’ar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!