Labarai
Yajin aiki: Za mu shiga tsakani don sulhuntawa, ku ci gaba da kasuwancin ku – Chidari
Majalisar dokokin Jihar Kano ta buƙaci matuƙa baburan adaidaita sahu da su janye yakin aikin da suke yi.
Shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ne ya bayyana hakan a wani saƙon murya da ya aikowa Freedom Radio.
Ya ce, majalisar dokoki ta lura da yadda al’ummar jihar Kano ke cikin wahala ta rashin abin hawa sakamakon yajin aikin.
“A matsayin mu na masu yin doka ba zamu zuba ido haka kawai ba, don haka mun shiga tsakiya tsakanin hukumar KAROTA da ƙungiyar ƴan adaidaita sahu don samun daidaito”.
“Muna kira da a ajiye makami a fito a ci gaba da harkokin sufuri domin sauƙaƙawa al’ummar Kano kafin mu zauna a warware matsalar cikin sauƙin” a cewar Chidari.
Injiya Hamisu Ibrahim Chidari ya sha alwashin ganin an mayar wa da duk wani ɗan adaidaita sahun da aka karɓi kuɗin sa ba bisa ƙa’ida ba.
Wannan dai na zuwa yayin da aka shafe kwanaki biyu ana cikin yajin aikin matuƙa baburan adaidaita sahu wanda ya gurgunta harkokin sufuri a Kano
You must be logged in to post a comment Login