Labarai
Yajin aikin : ASUU zata karbi Naira biliyan 30 daga gwamnati
Gwamnatin Najeriya ta amince ta biya kungiyar malaman jami’o’in kasar ASUU naira biliyan 30 a matsayin kudaden alawus.
Sai dai, Za’a soma biyan su kudaden ne daga watan mayun badi zuwa fabarairun shekarar 2022.
Zalika gwamnatin kasar za ta kashe naira biliyan 20 wajen farfado da bangaren ilimi a wani mataki na kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta kwashe watannin 6 tana yi yanzu haka.
Wadannan dai na daga cikin yarje-jeniyoyin da bangarorin 2 suka cimma a zaman dasukayi jiya Alhamis.
SSANU da NASU za su tsunduma yajin aikin makwanni biyu
Ba za mu dena yajin aiki ba sai gwamnati ta biya mana bukatun mu – ASUU
Ministan kwadago na kasar Chris Ngige, ya bayyana kwarin gwiwa kan yuwar Janye yajin aikin.
Anasa bangaren shugaban kungiyar malaman jami’o’in Najeriyar Biyodin Ogunyemi, yace akwai bukatar jama’a su kalli matsalolin da jami’o’in kasar ke fuskanta da idon basira domin yin wani abu akai.
You must be logged in to post a comment Login