Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

‘Yan bangar siyasa sun kaiwa Kwankwaso hari

Published

on

Wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne sun kai wa kwanbar motocin tsohon ministan tsaro kuma gwmanan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a nan Kano.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai magana da yawun dan takarar gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP Ibrahim Adam ya fitar cewa an kai wa kwanbar motocin Kwankwason hari ne a kusa da wani Otal a nan jihar Kano.

‘Yan bangar dai sun lalata motoci uku daga cikin jerin motocin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A dai jiya ne jam’iyyar PDP ta kammala zaben cikin gida bayan da uwar jam’iyyar PDP ta bayyana cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso shi ne jagoran jam’iyyar a nan Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!