Labarai
‘Yan bijilanti a Kano sun Kama Wani shahararren ‘dan damfara a Kano
- Wanda aka kama din dai ana zarginsa da damfarar wasu mutane.
- Kwamandan ya ce shekara guda kenan ana neman mai laifin da aka kama.
- Wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
Kungiyar bigilanti a jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Ibrahim Dauda bisa zarginsa da damfarar mutane.
Kwamandan rundunar da ke yankin Unguwa Uku Limawa kwanar Makabarta a karamar hukumar Tarauni Salisu Mai Jama’a, shi ne ya bayyana hakan da yammacin jiya juma’a.
Wanda yace tsawon shekara guda rundunar tana neman matashin kafin ya fada komarta.
Kwamandan ya kara da cewa ‘matashin da ake zargi ya tabbatar da aikata laifin da ake zarginsa da shi’.
Mai Jama’a ya kuma ce ‘yanzu haka zasu mika wanda ake zargin ga rundunar Yan sanda domin fadada bincike kan lamarin.
RAHOTO: Abdulkadie Haladu Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login