Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NNPC ya sanar da shirinsa na fara hakar rijiyar Mai a Jihar Nassarawa

Published

on

  • Kamfanin Mai a Nijeriya zai fara hakar rijiyar mai a Jihar Nassarawa.
  • Shugaban Kamfanin Malam Mele Kyari ne ya bayyana hakan.
  • Anasa ran fara hakar rijiyar man a watan Maris din shekarar 2023.

Kamfanin mai Nijeriya NNPCL ya sanar da shirin hakar rijiyar mai na farko a jihar Nassarawa.

Shugaban Kamfanin, Malam Mele Kyari, ne ya bayyana hakan yayin da Gwamnan Jihar, Engineer Abdullahi Sule, ya jagoranci wata tawaga ta fitattun ‘yan asalin Jihar Nassarawa a ziyarar ban girma da suka kaiwa kamfanin NNPC a Abuja.

Kyari, ‘ya ce sakamakon binciken da aka gudanar ya tabbatar da kasancewar albarkatun iskar carbon mai yawa a jihar Nasarawa’.

A watan Maris din shekarar da muke ciki ne ta 2023 ake sa ran za a fara aikin hakon man.

By:Abdulkadir Haladu Kiyawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!