Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Za mu daga darajar asibitocin karkara zuwa na kwararru – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar kano tace za ta daga darajar kananan Asibitocin da suke masarautun jihar 5 zuwa asibitin kwararru a kowanne yankin domin samar da kyakkyawar kulawa ga al’ummar jihar Kano.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Dr Aminu Ibrahim tsanyawa ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar Freedom da shirin ya mayar da hankali kan yadda za’a gyara harkokin lafiya.

Tsanyawa ya ce gwamnati a yanzu na kan matakin kara daukar ma’aikatan lafiya domin tallafawa wadanda suke karkara da kuma sauran kananan asibitocin jihar Kano.

Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya kara da cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar Kano zata dauki ma’aikatan lafiya domin inganta bangaren kiwon lafiya.

Ya kuma ce gwamnati na sane da irin kalubalen da kauyukan jihar nan ke fuskanta, musamman na rashin asibitoci da cibiyoyin lafiya a kusa da su, yana mi cewa nan ba da dadewa ba za’a gyara dukkan wani bangaren da ake da shi na harkokin kiwon lafiya a karkara.

Kwamishinan lafiya Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce an samar da wani kwamiti da zai rika bibiyar mutanen da suke da korafi tsakanin ma’aikatan lafiya da kuma masu jinya domin samun daidaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!