Kaduna
‘Yan bindiga sun kashe shugaban Fulanin yankin Doka a Kaduna – Aruwan
Wasu da ake zargin ‘Yan bindiga ne sun kashe wani shugaban Fulani a yankin Doka da ke karamar hukumar Kajuru, a jihar kaduna Alhaji Lawal Musa, wanda aka fi sani da Alhaji Maijama’a.
Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya tabbatar da faruwar lamarin a daren jiya Litinin 22 ga watan Mairs.
Ya ce wasu ‘yan fashi sun kashe Alhaji Lawal Musa a gaban danginsa a ranar Lahadin da ta gabata.
Kwamishinan ya ce, Alhaji Lawal Musa ya kasance shugaban al’ummar Fulani a cikin babban yankin nasu kuma ya yi aiki kafada da kafada da sauran shugabannin al’ummar wajen kokarin samar da zaman lafiya.
A cewer sa marigayin na zaune da dan uwansa Alhaji Gide Musa, kwatsam sai maharan suka bullo tare da bude musu wuta, lamarin da yayi sanadiyyar tserewar Alhaji Gide Musa wanda hakan ya basu damar yi masa yankan rago.
You must be logged in to post a comment Login