Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kimiyya

Gwajin Makami Mai Linzami: Amurka ta gargadi Korea ta Arewa da ta guji takalar fada

Published

on

Shugaban kasar Amurka Mista Joe Biden ya gargadi kasar Korea ta arewa da ta guji tsokanar kasar sa domin kuwa Amurka a shirye ta ke da ta mai da martani.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kasar ta Korea ta arewa ta yi gwajin wasu makamai masu linzami masu dogon zango guda biyu.

Ya ce ci gaba da takalar fada da kasar Korea ta arewa ke yi lamari ne da kasar Amurka ba za ta lamunta ba.

Kalaman mista Biden yasha bamban da na wanda ya gajeshi mista Trump wanda ya yi amfani da hanyoyin diflomasiya don sasanta sabani da ke tsakanin Amurka da Korea ta Arewa.

A jiya alhamis ne dai kasar Korea ta Arewa ta yi gwajin wasu muggan makamai masu linzami guda biyu a gabashin tekun Japan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!