Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan Bindiga sun sace matar Dagaci da dansa a Kano

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu iyalan gidan Dagacin kauyen Nasarawa da ke karamar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da matarsa Halima Kabiru, mai shekaru 38 da dansa Dahiru Kabiru, mai shekaru 20.

Jaridar Internet ta Solacebase ta ruwaito, Kwamishinan ‘yan sanda jihar Mamman Dauda, ne ya tabbatar rahoton sace mutanen.

“A ranar 2 ga Afrilu, da misalin karfe 12:45 na dare mun samu labarin cewa,  wasu ‘yan bindiga bakwai sun kai farmaki gidan Dagacin Nasarawa inda suka yi garkuwa da matarsa ​​da dansa.

“Masu garkuwa da mutanen sun boye wadanda suka dauke din zuwa wurin da ba a kai ga ganowa ba.

“Bayan samun bayanin, nan da nan muka tura tawagar ceto a ofisoshinmu da ke kusa da wurin, sannan muna tattaunawa da tawagar inda suke yin aiki tukuru don ceto wadanda lamarin ya shafa ba tare da sun ji rauni ba,” inji shi.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa za a kubutar da wadanda aka sace din tare da kama wadanda suka yi garkuwa da su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!