Kiwon Lafiya
‘yan bindiga sun sace tare da yin garkuwa da wasu fasinjoji a garin Fatakwal
‘Yan bindiga sun sace tare da yin garkuwa da fasinjojin wata mota da ta tashi daga garin Abua zuwa garin Fatakwal a jihar Rivers.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a jiya laraba a daidai mahadar hanya ta Rumuekpe da ke yankin karamar hukumar Emohua a jihar ta Rivers.
Wani shaidan gani da ido ya shaidawa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun yi kofar rago ne ga motar bayan sun fito daga cikin daji, sannan su ka fara harba bindiga sama.
Ya kuma ce bayan sun tsorata mutanen da ke daf da wajen da lamarin ya faru ne, sai suka tasa keyar fasinjojin goma tare da direban su zuwa cikin daji da ke kusa da wajen da lamarin ya faru.
Sai dai anata bangaren rundunar ‘yan sanda a jihar Rivers ta bakin mai magana da yawunta, Nnamdi Omoni, ta ce har ya zuwa yanzu ba ta samu labarin faruwar lamarin ba.