Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan bindiga sun sako dalibai 32 na makarantar Bethel Baptist dake Kaduna

Published

on

Yan bindigar da su kayi garkuwa da daliban makarantar Bethel Baptist dake karamar hukumar Chukun a jihar Kaduna sun sako dalibai 32 daga cikin dalibai 63 da suka rage a hannun su.

Sai dai har yanzu gwamnatin jihar ta Kaduna da jami’an ‘yan sandan jihar basu samar da sakin daliban ba.

Gidan Talabijin na Channels ya tabbatar da cewa daya daga cikin jagororin makarantar ta Bethel Baptist ya tabbatar mata da cewa an sako daliban.

A ranar 5 ga watan Yulin shekarar da muke ciki ta 2021 ne dai ‘yan bindigar suka kutsa cikin dakin kwanan daliban makarantar suka kuma tafi da dalibai 121.

Inda a ranar 25 ga watan Yulin ‘yan bindigar suka saki dalibai 28 bayan biyan kudun fansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!