Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mai horas da Rivers United

Published

on

An sace mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Rivers United Stanley Eguma tare da masu taimaka masa mutum biyu a kan hanyar Enugu.

Rahotanni na cewa, lamarin ya afku ne yayin da suke komawa gida bayan wasan da kungiyar su ta buga da Adamawa United a gasar cin kofin kwararru ta kasa.

Kungiyar ta Rivers United dai ta fafata da Adamawa United ne a ranar Lahadi 13 ga watan Yunin 2021, a filin wasa na Ribadu Square da ke Yola a jihar Adamawa.

Wannan dai ba shine karo na farko da aka fara yin garkuwa da ‘yan wasan kwallon kafa da masu horas da su a kasar nan ba.

Koda a watan Fabrairun da ya gabata ma sai da aka yi garkuwa da direban ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Adamawa United Kabiru Muhammad, wanda saida aka biya naira Miliyan daya sannan suka sake shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!