Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Mun hana cin gashin kai ga kowace hukumar wasanni – Dare

Published

on

Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare ya ce babu wata hukuma dake cin gashin kanta a karkashin ma’aikatar wasanni ta Najeriya.

Dare ya yi wannan gargadin ne yayin da yake kaddamar da sabon zababben shugaban hukumar guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa AFN Tonobok Okowa a Abuja.

Ministan ya ce baya goyon bayan yadda shugabancin hukumar AFN ya dare gida biyu tare da gudanar da zabe daban-daban a ranar Litinin 14 ga watan Yuni.

An gudanar da mabanbantan zabukan biyu a Abuja da Birnin Kebbi inda aka zabi Tonobok Okowa a matsayin shugaban tsagi guda na hukumar, yayin da a daya bangaren kuma aka zabi Shehu Gusau.

“Domin gudun rudani, babu wata hukumar wasanni da aka sahale wa cin gashin kanta kowace na a karkashin ma’aikatar wasanni ta kasa, “ inji Dare.

Dare ya kuma ce, “Mun jaddada amincewar mu da Tonobok Okowa a matsayin sabon zababben shugaban hukumar AFN a yanzu.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!