Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a jihar Niger

Published

on

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane ashirin a yankin karamar hukumar Shiroroo da ke jihar Niger

Wannan na zuwa ne awanni bayan da wasu ‘yan bindigar suka kai makamancin wannan harin a garin Kagara shalkwatar karamar hukumar Rafi a jihar ta Niger.

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne a kauyen Adagbi da ke mazabar Galkogo da safiyar yau alhamis.

Shaidun gani da ido sun shaidawa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun shigo kauyen ne akan babura tare da yin harbi sama kafin daga bisani su sace mutanen wadanda akasarinsu mata ne.

Sai dai har ya zuwa yanzu, rundunar ‘yan sandan jihar ta Niger ba ta fitar da sanarwa kan batun ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!