Labarai
Yan bindiga sun yi wa jami’an tsaro kwanton bauna a Kebbi

Akalla sojoji 11 da jami’in ‘yan sanda guda 1 ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun yi musu kwanton bauna a kauyen Giro Masa da ke karamar hukumar Shanga a jihar Kebbi.
Harin dai ya faru ne a daren ranar Talata inda jami’an tsaro da ake kyautata zaton sun dade suna gudanar da ayyukansu a yankin, suka gano ‘yan bindigar a farfajiyar wani kamfanin gine-gine.
Bayan da aka samu labarin an tura sojoji domin su tsare wurin amma yan bindigar sunyi musu kwanton bauna a hanya, inda Jami’in dan sanda da sojoji sun rasa rayukansu a harin tare da kona motocin sojoji biyu.
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ziyarci wadanda suka jikkata a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Birnin Kebbi. Bayan ziyarar, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin tausayi.
You must be logged in to post a comment Login