Addini
‘Yan boko haram 4000 sun tsere daga bakin daga – Rahoto
Wani rahoto da cibiyar bincike kan harkokin tsaro ta fitar, ya nuna cewa akalla mayakan Boko haram dubu hudu ne suka tsere daga bakin daga.
Rahoton ya kuma ce wannan adadi ya nuna , akwai baraka babba a bangaren ‘yan ta’addar.
A cewar rahoton wadanda suka tseren sun fito ne daga kasashen Kamaru, Chadi, Jamhuriyar Nijar da kuma nan Najeriya.
‘Yan kungiyar Boko haram dai sun kwashe tsawon shekaru goma suna tabka ta’asa a yankin tabkin Chadi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Rahoton mai shafuka 28 ya ce, wadanda suka tseren wasunsu shun shiga kungiyar ta boko haram ne a kashin kansu, yayin da wasunsu kuma satosu aka yi aka tursasu shiga.
Cibiyar ta cikin rahoton ta kuma bayyana tsoron mutuwa, yunwa da rashin tabbas a matsayin wasu daga cikin dalilan da ya sa suka tsere.
Ko da ya ke rahoton ya ce zai yi matukar wuya a gano cikakken adadin wadanda suka tseren, amma alkaluman da cibiyar ta tattara ya nuna cewa, guda dubu biyu da dari hudu ‘yan kasar Chadi ne, yayin da wasu dubu daya ‘yan Najeriya ne.
Sai dari biyar da tamanin da hudu ‘yan kasar Kamaru da kuma dari biyu da arba’in da uku ‘yan kasar Jamhuriyar Nijar.
You must be logged in to post a comment Login